Yawancin ‘yan gudun hijirar dai sun fito ne daga ‘kauyukan Konduga, tun shekaru biyu zuwa uku da suka gabata, sakamakon hare haren da ‘ya ‘yan kungiyar Boko Haram sukan kai musu a baya wanda da yawansu suka kwarara zuwa cikin garin Maiduguri, yayin da wasu ke samun mafaka a sansanin ‘yan gudun hijira, wasu kuma a gidajen ‘yan uwa da abokan arziki.
Karamar hukumar Konduga na daga cikin kananan hukumomin da mayakan kungiyar Boko Haram suka mamaye a baya, duk da cewa mayakan sun sha fafatawa da rundunar sojan Najeriya a garin na Konduga kuma basu sami damar kwace garin ba, sai dai baki ‘daya kauyukan garin sun fada hannun mayakan, daga bisani ne ma rundunar sojan Najeriya ta sake kwato su.
Da yawa daga cikin ‘yan gudun hijirar sun shaidawa wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda, cewar sun shirya komawa gidajensu sun kuma mika godiyarsu ga Allah da kuma gwamnan jihar da duk wadanda suka taimaka musu. Yawancin su dai sunce sun kwashe kusan shekaru uku suna gudun hijira.
Gwamnan jihar Borno Kashin Shettima, ya sha jaddadawa manema labarai yana mai fatan cewa zuwa karshen wannan shekarar zasu rufe dukkannin sansanonin ‘yan gudun hijira da ke fadin jihar, don ci gaba da mayar da jama’a zuwa garuruwansu da kuma sake gina garuruwan da ‘yan Boko Haram suka kona.
Saurari cikakken rahotan Haruna Dauda daga Maiduguri.