Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar kasafin kudin bana daga majalisar dokokin jihar Borno, da kakakin majalisar Abdulkarim Lawan y ya kima masa a fadar gwamnatin jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa, bai gamsu da kokarin da yace kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya suke yi ba, domin bisa ga cewarshi, yawan kudin tallafin da suke badawa yana tafiya ne a kansu, ya bada misali da cewa, zaka ga sun gina bandaki biyar a garin Goza amma su tashi a jirgi mai saukar angulu sau bakwai.
Gwamna Shatimma yace bisa wannan dalilin zasu rufe dukan sansanan ‘yan gudun hijira a jihar ranar ashirin da tara ga watan Mayu mai zuwa, domin mutane su koma gidajensu su ci gaba da rayuwa cikin mutumci.
Gwamnan ya bayyana matsalolin dake addabar jihar a matsayin “matatsa” da kowa ke zuwa da sunan taimako amma basu gani a kasa. Yace akwai wadanda ke zuwa jihar su kama gidajen haya na tsawon shekaru kamar suna fatar matsalolin su ci gaba.
Ga cikakken rahoton da wakilinmu a jihar Borno Haruna Dauda Bi’u ya aiko mana.