Tawagar dai ta fara ne da ziyartar sansanin ‘yan gudun hijira dake garin Dalori, inda aka ce ana da ‘yan gudun hijira fiye da 37000 da marayu fiye da 6000 da kuma matan da suka rasa mazajensu fiye da 5000 dukkansu sun fitone daga karamar hukumar Bama, wadda yanzu haka gwamnati da gidauniyar Dan Gote suka dukufa wajen sake gina musu garuruwansu.
A jawabin gwamna Shettima, yace dole ne su baiwa yaran ilimi don abu ne mai muhimmanci, idan babu shi ba zamu cimma nasarar abin da muke so mu cimma ba. shima Alhaji Aliko Dan Gote, yayiwa ‘yan gudun hijira jawabi wanda suka hada da mata da yara kuma yayi alkwarin taimaka musu wajen gudanar da rayuwarsu.
Domin karin bayani.