Alhaji Aliko Dangote attajirin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka ya kaddamar da rukunin wasu gidaje dari biyu da suka lakume Naira biliyan daya ga wasu mata ‘yan gudun hijira da suka rasa mazajensu a jihar Borno sanadidiyar rikicin Boko Haram.
Alhaji Dangote ya soma aikin gidajen ne tun daga lokacin da matan suka rasa mazajensu yayinda sansanin ‘yan gudun hijira ya cika makil dalili ke nan da ya bada tasa gudummawar domin taimakawa wadanda rikicin ya daidaitasu.
Kamfanin Dangoten ya kaddamar da gidajen ne tare da taimakon gwamnan jihar Kashim Shettima.
Wasu matan da suka anfana da gidajen sun bayyana jin dadinsu. Esther Ishaku Kachalla mai ‘ya’ya shida wadda ta samu gida ta ce maigidanta aka kashe amma gashi an zo rabon gidajen gwamnan jihar bai duba banbancin addini ko kabila ba. Ya share mata hawaye, ita da ‘ya’yanta. Daga gidan haya ta fito inda kawo yanzu ma ana binta kudin hayan saboda bata da aiki.
Akwai wata mai ‘ya’ya takwas da ita ma aka bata gida. Ta yi matukar godiya tare da bayyana farin cikinta.
Dangane da abun da ya sa Aliko Dangote ya dauki nauyin gina gidajen, attajirin ya bayyanawa Muryar Amurka cewa ya ji “gwamnan jihar yana kokarin ginawa mutanen gidaje saboda bala’in da suka shiga. Sai muka shigo mu taimaka. Tun can farko mun bada kudi kimanin Naira biliyan bakwai. Shekaru biyu da suka gabata gwamnan ya kuduri anniyar ginawa mutanen gidaje. Nan take kamfaninmu ya yi alkawarin taimakawa da Naira biliyan biyu”
A cewar Alhaji Dangote gwamnan jihar Borno ya fito karara ya ce baya son tsaabar kudi, maimakon hakan a bashi kayan gina gidaje da kudin zai saya.
Matakin da gwamnan ya dauka ya fi domin a cewar Dangote da an bada kwangilar gina gidajen da an kashe fiye da Naira biliyan uku.
Duk da wadannan gidajen da aka gina da kudi Naira biliyan daya Dangote ya sanar da ci gaba da gine ginen da Naira biliyan daya da ya ragu cikin biyun da ya yi alkawari
Gidaje dari biyun da aka gama aka kuma raba, kowanne nada gidan kiwon kaji da kiwon kifi da ma wurin gashin kifin da wurin shuka. Bugu da kari Dangote zai ba kowace mace da aka ba gida Naira dubu dari daya.
A saurari rahoton Haruna Dauda da karin bayani
Facebook Forum