A cewar gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, yace yana sa ran nan ba da dadewa ba za a rufe dukkannin sansanonin ‘yan Gudun Hijira dake fadin jihar, da kuma mayar da jama’a zuwa garuruwansu. Sai yace babu tilastawa ga duk wanda baya son ya komawa inda ya fito ba.
Da yake bayani Gwamna Shettima yace “Aniyarmu a gwamnatance itace muna son muga dukkan mutanenmu sun koma garuruwansu a ranar 29 ko kuma kafin 29 ga watan Mayu. Yanzu inda muka sa gaba shine garin Bama, don idan zamu gyara garin Bama da Goza zamu iya cewa mun gance rabin matsalar dake addabarmu a jihar Borno.”
Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda, ya ziyarci cikin garin Bama don ganewa idanunsa yadda ake gudanar da ayyukan, inda ya tarar ana ci gaba da ayyuka da kuma share garuruwan. Ya kuma zanta da wasu ma’aikata wanda suka tabbatar masa cewa komai na tafiya bisa tsari, kuma suna ganin zasu iya kammala aikin cikin wa’adin da aka daukar musu.
Garin bama dai na daga cikin garuruwan da rundunar sojan Najeriya ta kwato daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram a shekarar da ta gabata.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Haruna Dauda daga garin Bama.