Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ana Kokarin Nemo Yan Mata 3 Da Akayi Garkuwa Dasu A Lagos


Yan Makaranta rike da tutan Najeriya a Lagos, lokacin bikin cika shekaru 55 da samun yancin Najeriya.
Yan Makaranta rike da tutan Najeriya a Lagos, lokacin bikin cika shekaru 55 da samun yancin Najeriya.

Gwamnatin jihar Lagos tare da hadin kan jami’an tsaro na kokarin ganin an kubutar da yan matan nan guda 3 da wasu yan bindiga suka sace a wata makarantar kwana, dake garin Ikorodu a Lagos.

Kwanaki uku kenan dai da sace yan matan, dake karatu a makarantar kwana dake Ikorodu. Yanzu haka dai masu garkuwa da yan matan, sunce suna bukatar kudin fansa har Naira Miliyan 200, daga hannun iyaye da hukumomin makarantar.

Mataimakin sefeto janal na yan Sandan Najeriya, Bala Hassan, yayi wakilin Muryar Amuraka karin haske kan batun, inda yace suna nan suna aiki domin ganin dawo da yan matan cikin koshin lafiya.

Sace yan matan 3 yazo ne a yan kwanaki kadan da cika shekara biyu da sace yan matan Chibok dake jihar Borno, wanda yan Boko Haram sukayi wanda kuma ake ci gaba da neman su ruwa a jallo.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG