Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Daruruwan ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Yankin Neja a Kan Babura


Wani yanki da 'yan bindiga suka kai hari.
Wani yanki da 'yan bindiga suka kai hari.

Matsalar Tsaro na kara ta'azzara a sassan Najeriya musamman a arewacin kasar inda a baya-bayan nan wasu mahara suka far wa yankin jihar Neja suka kashe wasu mutane.

Wasu daruruwan ‘yan bindiga su kimanin 200 dauke da manyan makamai akan babura sun kai hari a yankin Kamfanin Bobi da ke karamar hukumar Mariga ta jihar Nejan Najeriya.

Harin wanda hukumomin jihar suka tabbatar da aukuwarsa, ya faru ne da yammacin ranar Laraba.

Bayanan da Muryar Amurka ta tattaro sun nuna an tafka gumurzu a tsakanin jami’an tsaro da kuma wadannan ‘yan bindiga.

Wasu daga cikin mazauna garin na kamfanin Bobi sun ce an samu asarar rayuka ciki har da na jami’an tsaro da kuma 'yan banga.

“Sun harbi yaro guda a hannu, amma cikin mutanensu an kashe guda, sun harbi ‘yan sanda biyu sun kashe ‘yan banga biyu.” In ji wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa.

Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Nejan ya cutura domin Kwamishinan ‘yan sandan Adamu Usman da ma kakakin ‘yan sandan Wasiu Abiodun ba su dauki waya ba.

Amma gwamnatin jihar Nejan ta tabbatar da aukuwar lamarin.

“Har yanzu ba mu samu tabbacin ko an rasa rayuka ko ba a rasa ba, kuma ko an rasa ba mu san ko guda nawa ba ne.” In ji kwamishinan Labarai na jihar Alhaji Sani Idris.

Ya kara da cewa tuni aka tura karin jamt'an tsaro a yankin don tabbatar da maido da doka da oda.

A halin da ake ciki al’ummomin da ke zaune a wannan yanki na Arewacin jihar Nejar mai iyaka da jihohin Kebbi Zamfara da Kaduna suna zaune ne cikin wani yanayi na tsahin hankali a sakamakon yadda kusan kowane lokaci ‘yan bindigar ke auka masu.

XS
SM
MD
LG