Sarkin Musulmin ya yi wannan kiran ne a lokacin da wata tawagar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta ziyarce shi domin tattaunawa kan kaddamar da shirin taimaka wa ‘yan gudun hijira ta amfani da sashen Zakkah da Wakafi na hukumar.
Alkalumman hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya sun nuna akwai ‘yan gudun hijira da yawansu ya haura 500,000 a arewa maso yammacin Najeriya kadai wadanda ke cikin bukatar agaji duk da cewa hukumomi da kungiyoyi na iya kokarinsu wajen taimakawa.
Yanzu haka sashen kula da Zakkah da Wakafi na hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ya na kula da ‘yan gudun hijira da yawansu ya kai miliyan 80 a duniya kuma kashi 60 cikin 100 daga cikinsu su na a kasashen Musulmi.
A lokacin ziyarar da tawagar hukumar ta kai jihar Sokoto, mai alfarma Sarkin Musulmi ya nuna damuwa kan yawaitar ‘yan gudun hijira musamman kananan yara da aka maida marayu a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
“Akasarin marayun da muke da su kananan yara ne wadanda da yawansu su na arewa maso gabashin Najeriya,” a cewar Sarkin Musulmi. Ya kara da cewa, "na san majalisar dinkin duniya ta san da zaman su, babban abin damuwa shi ne yadda za a kula da wadannan yaran don akwai bukatar kara tashi tsaye domin kyautata rayukansu."
Jagoran tawagar Khalid Khalipha, ya ce sun je Sokoto ne don tattaunawa da hukumar Zakkah da wakafi a zaman babbar abokiyar hulda da kuma shi kansa mai alfarma Sarkin Musulmi.
“Mun tara makudan kudi a ‘yan shekarun da suka gabata, yanzu muna kan fadada ayyukan jinkai a kasashe ta yadda jama'a zasu ci gajiyar kudin, zamu kaddamar da babban shiri na yin aiki tare da hukumar Zakkah ta Sokoto domin yin cikakken amfani da kudin Zakkah ga al'ummar Najeriya,” a cewar Khalipha.
Muhammad Lawal Maidoki, shugaban zartaswa na hukumar Zakka da Wakafi a jihar Sokoto, ya ce idan wannan kawance ya samu nasara ana sa ran ya amfani ‘yan gudun hijira a Najeriya wadanda yawansu ke karuwa sanadiyyar ayyukan ta'addanci da suka dabaibaiye yankin arewacin Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir.