Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Farautar 'Yan Bindigan Da Suka Kashe Shugaban APC A Nasarawa


Shugaban Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu
Shugaban Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ce tana kan bincike don gano wadanda suka kashe shugaban jam'iyyar APC a jihar, Mista Philip Tatari Shekwo.

A daren ranar Asabar da ta gabata ne wadansu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka shiga gidan marigayin suka dauke shi, wanda daga bisani aka samu gawarsa a kusa da gidansa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, ASP, Ramhan Nansel, ya ce an sami gawarsa an kuma ajiye a asibiti ana kan bincike don gano wadanda suka kashe shi.

Sai dai ya ce ya zuwa yanzu ‘yan sanda ba su kama kowa dake da hannu a kisan ba tukuna. Ya kuma ce basu da wani bayani a kan dalilin da yasa aka yi garkuwa da shi kana aka kashe shi.

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta zuba jami’anta a cikin gari kana ta tabbatarwa al’ummar jihar cewa ba za a sake samun irin wannan danyen aikin ba kuma su kwantar da hankulansu.

Sakataren jam’iyyar APC a jihar Nasarawa, Alhaji Aliyu Bello ya ce sun kadu matuka da mutuwar shugaban jam’iyyar ta su. Ya ce da farko sun dauka masu garkuwa da mutane dan samun kudin fansa ne, har ma suna tunanin yanda za su kubutar da shi, sai kwatsam aka tsinci gawarsa.

Alhaji Bello ya ce abin bakin ciki ne irin wannan abu na faruwa a cikin Najeriya, ya ce yanzu sun bar jami’an tsaro su yi aikinsu, kana ya kyautata zaton asirin wadanda suka aikata danyen aikin zai tonu.

Wani kusa a jam’iyyar APC a jihar ta Nasarawa, Alhaji Sidi Ndagi ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki daya bada gudunmawa wajen samun nasarar da jami’iyyar tasu ta yi a jihar.

Ga rahoton Zainab Babaji daga Jos:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG