Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manoman Alkama a Najeriya Sun Koka


Gonar Alkama.
Gonar Alkama.

Manoman sun koka ne kan yadda gwamnatin kasar ta mayar da su saniyar ware a shirin ta na Anchor Borrower da aka tsara domin tallafa wa manoman shinkafa da alkama da nufin bunkasa kasa da abinci.

A Shekara ta 2016 ne gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani shiri na musamman da ta yi wa lakabi da Anchor Borrower wanda a karkashinsa ta kudiri aniyar bunkasa noman alkama da shinkafa a kasar.

Hakan ya biyo bayan matakin da hukumomin Najeriya suka dauka na hana shigar da shinkafa kasar daga kasashen ketare.

Babban bankin Najeriya na CBN shi ke daukar nauyin samar da kudade da kayayyakin aiki domin tallafa wa manoman, inda ya zuwa yanzu gwamnati ta kashe biliyoyin naira wajen aiwatar da wannan shiri.

To sai dai, manoman alkama a Najeriya na kokawa kan yadda suka ce bankin na CBN da sauran masu ruwa da tsaki suka mayar da su saniyar ware wajen aiwatar da shirin na Anchor Borrower, duk kuwa da gundunmawar su ga sha’anin samar da abinci a kasa.

Alhaji Salim Sale, shugaban kungiyar manoman alkama a Najeriya, ya ce a shekarar nan ta 2020, sun tura mutane 287,000 da suka yi niyar yin noman alkama amma akalla mutane 25,000 kadai aka dauka a karkashin shirin, duk da cewa ana amfani da alkama sosai a kasar ta hanyoyi dabam-daban.

A nasu bangaren, manoman shinkafa sun ce sun daura damara domin tunkarar aikin noman shinkafar rani.

Alhaji Ado Alhassan Yakasai, da ke zaman sakataren kungiyar masu noman shinkafa ta kasa reshen jihar Kano, ya ce shirin gwamnati na Anchor Borrower na haifar da alfanu a garesu duk kuwa da kalubalen da suka fuskanta a baya.

Tuni dai masu kula da al’amura a fagen aikin noma a Najeriya, ke nanata bukatar bai wa bangaren noma kulawar da ta dace kafin kasar ta cimma burinta na wadata al’umarta da abinci ba tare da tallafi daga ketare ba.

Saurari karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00


Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG