Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki Wasu Daga Cikin 'Yan Sandan Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Katsina


Jami'an 'yan sanda sun tsaya kuwa da sakateriyar gwamnatin tarayya a Abuja
Jami'an 'yan sanda sun tsaya kuwa da sakateriyar gwamnatin tarayya a Abuja

Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu daga cikin ‘yan sandan nan da aka yi garkuwa da su a yankin jihar Katsina sun samu kubuta.

‘Yan sandan su 12 na kan hanyarsu ne ta zuwa wani aiki na musamman da aka tura su a jihar ta Zamfara.

Bayanai sun yi nuni da cewa ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su sun nemi kudin fansa kafin su sake su.

Amma babu wata kafa ko majiya da ta nuna cewa an biya kudin fansa kafin sakin wasu daga cikin ‘yan sandan.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kai ‘yan sandan wani asibiti da ke Gusau babban birnin jihar domin a duba lafiyarsu.

Ya zuwa yanzu hukumomin tsaron kasar ba su ce uffan ba dangane da wannan al’amari ba, amma wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa an saki wasu daga cikin ‘yan sandan.

Bayan da aka samu rahotanni garkuwa da ‘yan sandan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya fito ya kalubalanci gwamnatin Najeriya.

“Kamar kowa, ni ma ina cikin damuwa dangane da cewa jami’an tsaro 12 da ya kamata su tsare lafiyarmu da dukiyoyinmu sun fada tarkon masu garkuwa da mutane. Ya kamata a yi duk abin da za a yi domin kubutar da su.” Atiku ya ce a wani sakon Twitter da ya wallafa.

Najeriya dai ta fada kangin masu garkuwa da mutane musamman a arewacin kasar inda ko a farkon makon nan wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wani ayarin daliban Jami’ar Ahmadu Bello da ke kan hanyarsa ta zuwa wani taro a Legas.

Hukumomin Najeriya sun ce suna daukan duk matakan da suka dace wajen ganin sun shawo kan wannan matsala, inda aka tura jami’an tsaro zuwa yankunan Zamfara, Katsina da Sokoto da matsalar ta fi kamari don dakile ayyukan ‘yan bindigar.

XS
SM
MD
LG