Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BORNO: Kungiyar Boko Haram Ta Yiwa Wasu Yankan Rago


Irin barnar da 'yan Boko Haram suke yi
Irin barnar da 'yan Boko Haram suke yi

Har yanzu kungiyar Boko Haram na cigaba da hallaka mutane ko ta kunar bakin wake ko ta harbesu ko kuma ta yankasu kamar rago musamman a jihar Borno.

Kungiyar Boko Haram tana cigaba da tsananta aikin ta'adanci musamman a jihar Borno. Cikin wannan makon kadai ta hallaka mutane kusan dari biyu.

Shekaran jiya Laraba ta shiga masallatai gaf da lokacin da mutane zasu fara sallar isha ta kashe mutane kusan dari a garin Kukawa dake jihar Borno. Yanzu dai garin ya zama kufai domin mutane sun watse zuwa wasu wuraren.

Ana juyayin abun da ya faru ranar Laraba sai gashi yau kungyar ta yiwa wasu mutane goma sha daya yankan rago a jihar Bornon. Kungiyar ta zargi mutanen da yiwa mahukuntan Najeriya leken asiri lamarin da tace yana yi mata zagon kasa.

'Yan ta'adan sun shiga garin Miringa inda suka je gida gida suna zakulo mutane. Sun shiga masallaci inda ake salla sun fitar da mutane goma sha daya kana suka yankasu kamar raguna.

Wannan shi ne karo na biyar a wannan makon da kungiyar zata kai hari da kawo yanzu ya lakume rayuka fiye da 173. Da alama kungiyar tana bin umurnin ISIS ne kungiyar da ta yi ikirarin kafa daular Islama a yankunan Syria da Iraqi da Boko Haram din ta yiwa muba'aya.

Wannan kungiyar ta'adanci da aka lakabawa Boko Haram tana fafitikar kafa daular Islama ne a arewacin Najeriya bisa ga nata fahimtar shari'ar musulunci. Kawo yanzu kimanin mutane 13,000 suka halaka da suka hada da musulmai da kiristoci. Kungiyar ta kwashi shekaru shida tana wannnan aika aikar. Akwai wasu miliyan daya da rabi da suka rasa muhallansu sanadiyar ta'adancin kungiyar.

XS
SM
MD
LG