Jama'a sun fito yin zanga zanga ne domin nuna rashin amincewar su da aniyar shugaban kasar na fitowa tsayawa takara a karo na uku.Haka kuma Amurka ta ce akwai kurakurai a cikin zaben ‘yan majalisun da akayi.
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar a jiya Alhamis tace, shawarar da Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya yanke na fitowa takara karo na uku, ta yi sanadiyar mutawar mutane dayawa, da tilastawa ‘yan kasar Burundi sama da dubu 144 gudu zuwa kasashen makwabta, harma da janyo tabarbarewar tattalin arzikin kasar.
Gwamnatin ta Amurka tace shawarar gwamnatin Burundi na cigaba da zaben ‘yan majalisun da akayi 29 ga watan Yuni, duk kuwa da cewa babu wani zaman lafiyar da za’a iya gudanar da zaben, ya kara dagula lamarin. Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bukaci gwamnatin ta Burundi da ta saurari kiranye-kiranyen da kasashe ke yi mata na ta dakatar da zaben shugaban kasar da aka shirya yi 15 ga wannan watan.