Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Miyagu Sun Sace Wani Hamshakin Dan Kasuwa A Taraba


Sufeto-Janar na 'yansandan Najeriya Solomon Arase
Sufeto-Janar na 'yansandan Najeriya Solomon Arase

Yayin da aka sace wani babban dan kasuwa a jahar Taraba, a jahar Adamawa kuwa damke masu aikata irin wannan danyan aikin aka yi

A cigaba da barazana ga tsaro a arewa maso gabashin Najeriya, wasu yan bindiga da ba’a san ko su waye ba,sun kai hari Mararrabar Ba’isa a kudancin jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya, inda suka yi awon gaba da wani mashahurin dan kasuwa wanda kawo yanzu ba’a san inda aka yi da shi ba. Wannan al’amarin ya haddasa fargaba da rashin sanin tabbas tsakanin al’ummar yankin.

Wani wanda ya nemi a sakaya sunansa ya gaya ma wakilinmu Ibrahim Abdul’aziz cewa iyalan wanda ake wa lakabi da “Esaiko” da miyagun sun shiga tattaunawa kan kudin fansa, wanda ya kai Naira miliyan 50. Y ace rashin kai dauki daga jama’a da jami’an tsaro cikin lokaci mai yiwuwa na da nasaba da faruwar abin da dare. Shi kuwa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba DSP Joseph Kwaji ya shaida ma wakilin namu cewa tuni aka baza jami’an tsaro don bincike. Ya yi kira ga jama’a da su sa ido su fallasa miyagun da kan shiga cikin jama’a da niyyar cuta.

A wata sabuwa kuma ‘yan sintiri na kungiyar Fulani ta Tabital Fulaku shiyyar jihar Adamawa ta wadda kan taimaka ma jami’an tsaro, ta damke wasu barayin shanu da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa. Wani jigo a kungiyar ta Tabital Fulaku Alhaji Aliyu Nuhu ya bayyana cewa sun mika miyagun ga ‘yan sandan ciki na CID ana ta bincikensu. Wani dan gidan Ali Kwara, wanda ya jagoranci kama barayin shanun y ace ya gaya ma Ali Kwara halin da ake ciki shi ne ya hada shi da wani babban jami’in tsaro wanda ta haka su ka yi nasarar kama miyagun da bindigogin AK 47 guda biyu da harsasai 120 da dai sauransu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG