WASHINGTON, DC —
A wani gangami da bangaren sabuwar jam'iyyar ya yi a Yola babban birnin jihar Adamawa gwamna Murtala Nyako ya fito karara ya ce tsinewarsu ce ta kama shohuwar jam'iyyar.
A jawabinsa gwamnan Adamawa ya yi biris da kalamun Bamanga Tukur wanda ya yi jiya inda yake ikirarin tsige duk wadanda suka yi masa tawaye kuma wai zai sa dakarun tsaro su kamasu. Gwamnan ya ce sun daura damarar yaki da 'yan milkin kamakarya dake son dukusar da jam'iyyarsu.Ya ce sun fice ne gada tsohuwar jam'iyyar domin su kare mutuncinsu da zaman lafiyan Najeriya. Ya ce babu zaman lafiya idan ba adalci.
Shugaban sabuwar jam'iyyar bangaren Adamawa Alhaji Umaru Kugama ya tofa albarkacin bakinsa. Ya ce gwamnan Adamawa da wasu gwamnoni bakwai sun zagaya Najeriya sun tattauna domin su fitarwa al'umma 'yancinsu da samar masu da adalci. Ya ce burinsu shi ne cire duk masu mulkin danniya da kamakarya.
A jihar Taraba ma lamarin haka ya ke. Alhaji Ado Munmuni Baki shugaban reshen Taraba ya ce yadda jam'yyar ke tafiya idan aka cigaba da haka za'a je a hallaka ne gaba daya. To amma wadanda suka kafa jam'yyar tun can farko sun yunkura su cetota daga wadanda suke son hallakata.
To sadai wasu sun fara nuna shakku domin wai wadanda suka balle mutane ne da suke son mulki ko ta halin kaka. Har wayau wai su ne suka daure ma Jonathan gindi har ya zama shugaban kasa. Yanzu da tafiyarsu ta yi tsami wai dalili kenan dasuka shiga fadan cikin gida.Kokari suke su kwace mulki ba domin suna son jin dadin talaka ba ne.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.