A wata sanarwar da ta aikawa kafafen yada labarai a yammacin jiya Lahadi gwamnatin mulkin sojan kasar Chadi a ta bakin kakakinta General Azem Bermandoa Agouna ta yi watsi da dukkan wani shirin tanttaunawa da ‘yan tawayen kungiyar FACT.
Gwamnatin ta ce 'yan tawayen, mutane ne da suka aikata munanan laifika ga kasar Chadi a bisa la’akari da kisan sojojinta ciki har da shugaba Idriss Deby Itno.
Gwamnatin sojin ta bukaci hukumomin Jamhuriyar Nijar da su damka mata wasu shugabain ‘yan tawaye da take hasashen sun gudo garuruwan N’gourti da N’guigmi na jihar Diffa domin su gurfana gaban koliya.
Karin bayani akan: Idriss Deby, General Azem Bermandoa Agouna, Kanem, Jamhuriyar Nijar, kasar ta Chadi, da Chad.
Sai dai a ra’ayin wani kwamandan tsohuwar kungiyar MNJ ta ‘yan tawayen Nijar Ahmed Ouagayya, zama kan teburin sulhu ita ce hanya mafi a’ala wajen neman mafitar halin da Chadi ta shiga bayan rasuwar Idriss Deby.
Chadi da NijAr sun rattaba hannu akan yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin shari’a wacce a karkashinta kowacce daga cikin kasashen biyu ta dauki alkawarin taimakawa ‘yar uwarta idan bukata ta taso.
Amma mai nazarin al’amuran yau da kullum Moustapha Abdoulaye na ganin zabi ya rage wa shugaba Mohamed Bazoum.
Kawo yanzu gwamnatin Nijar ba ta bayyana matsayinta ba game da bukatar tisa keyar shugabanin ‘yan tawayen da hukumomin Chadi ke hasashen sun ketaro jihar Diffa ba.
Rahotannin safiyar yau Litinin sun ambato jagoran kungiyar FACT Mahamat Mahadi Ali ya na cewa har yanzu ya na yankin Kanem mai makwaftaka da Jamhuriyar Nijar kuma a shirye ya ke a ci gaba da kafsawa ganin yadda sojojin gwamnatin Chadi ke luguden wuta akan baradansa.
Saurari rahoto ckin sauti daga Souley Moumouni barma: