Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CHADI: An Nada Dan Marigayi Idriss Deby A Matsayin Shugaban Riko Na Soji


Mahamat Idriss Deby, Dan marigayi shugaban Chadi Idriss Deby.
Mahamat Idriss Deby, Dan marigayi shugaban Chadi Idriss Deby.

Rundunar sojin kasar Chadi ta nada dan marigayi Idriss Deby Itno, domin maye gurbin mahaifinsa a matsayin shugaban riko na mulkin soji.

Mahamat Idriss Deby babban jami'i ne a rundunar sojin kasar ta Chadi, kuma daya daga cikin 'ya'yan marigayi shugaba Deby da ke cikin rundunar sojin kasar.

Tuni dai da rundunar sojin kasar ta rusa gwamnati da majalisar dokoki, jim kadan bayan ba da sanarwar rasuwar shugaba Deby, to amma kuma ta sha alwashin gudanar da sahihin zabe tare da mayar da kasar kan turbar dimokaradiyya nan da watanni 18.

Haka kuma an kafa dokar hana fitar dare a duk fadin kasar, kana kuma aka ba da sanarwar rufe dukkan kan iyakokin kasar.

Karin bayani akan: Idriss Deby, Boko Haram, kasar ta Chadi, da Chad.

Mutuwar ta Deby ta zo wa ‘yan kasar a ba zata, kwana daya bayan da aka ayyana marigayin mai shekaru 68 a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar, wanda zai ba shi damar wa’adi na 6 a kujerar shugaban kasar.

Marigayi Shugaban Chadi, Idriss Derby
Marigayi Shugaban Chadi, Idriss Derby

Idriss Deby wanda soja ne, ya kasance shugaban kasar ta kasar ta Chadi mafi dadewa akan mulki, inda ya soma tun a shekarar 1990 sakamakon wani juyin mulki.

Sabon Shugaban Mulkin Sojin Chadi A Wajen Jana’izar Mahaifinsa

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG