Shugabanin kasashe akalla 10 ne suka halarci taron jana’izar shugaban kasar Chadi Idriss Deby cikinsu har da Mohamed Bazoum na Nijar da Felix Tchisekedy na RDC bugu da kari da shugaban rikon kungiyar tarayyar Afirka da kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Hakan na kara jaddada tasirin marigayin a nahiyar Afirka baki daya saboda jajircewarsa akan batun tabbatar da tsaro.
Lamarin da ya sa batun maye gurbinsa da mutumin da ya dace ke daukar hankalin jama’a a kasashe makwafta irinsu Jamhuriyar Nijar.
Shugaban kungiyar wanzar da dimokraradiya ta ROAD Son-Allah Dambaji na daga cikin wadanda ke jan hakulan masuruwa da tsaki a Chadi da su kasance tsintsiya madaurinki daya don ganin an kafa gwamnatin da kowane bangare zai yi na’am da ita.
Karin bayani akan: Idriss Deby, shugaban Faransa Emmanuel Macron, kasar ta Chadi, da Chad.
Sai dai shugaban kungiyar COAD Amadou Roufai Lawan Salao na cewa dole ne kasashen Afrika su yi wa al’ummar Chadi rakiya a wannan lokaci na neman mafitar rudanin da ake tunanin rasuwar Idriss Deby na iya haddasawa a nan gaba.
Dimbin mutane na ciki da wajen Chadi ne suka halarci taron jan’izar a N’djamena don yi wa marigayin ban kwanan karshe inda aka yi masa addu’oi da hidmomin karramawa a hukumance kafin daga bisani a damka gawarsa ga iyalansa wadanda suka nufi garinsu na asali Amdjaress da ke yankin Arewa maso gabashin kasar kusa da iyakar Sudan inda aka bizne shi.
Idriss Deby wanda ya shafe shekaru 30 ya na mulkin Chadi ya rasu ne a ranar Talatar 20 ga watan Afrilu bayan da ya ji rauni a lokacin da sojojinsa ke gwabza fada da ‘yan tawayen kungiyar FACT a cewar wata sanarwar rundunar mayakan kasar.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Sabon Shugaban Mulkin Sojin Chadi A Wajen Jana’izar Mahaifinsa