Shugabannin kasashe da dama, sun yi ban kwana na karshe da marigayi Shugaba Idriss Deby a wani biki da hukumomi suka shirya a N’Djamena babban birnin kasar a ranar Juma’a.
Yayin da yake jawabi, Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya jinjinawa takwaran aikinsa da ya rasu, kan irin rawar da ya taka a yaki da kungiyoyi masu ikrarin jihadi a yankin Sahel.
“Kana daya daga cikin mutane na farko da ke amsa kiran da kasashe ke yi a wannan yanki wajen kare nahiyar Afirka daga ‘yan ta’adda masu dauke da makamai a yankin Sahel a shekarar 2013. Ka kuma taimakawa kawayenka na Mali tare da yin aiki kafada da kafada da Faransa,” Macron ya fadawa masu halartar jana’izar, a wani jawabin da ya yi ga mutumin da ya kwatanta a matsayin “amintaccen aboki na hakika.”
Deby, mutum ne da ya kasance na hannun daman kasashen yammacin duniya a yaki da ake yi da masu ikrarin jihadi a Afirka, an ji masa mummunan rauni ne a wannan mako, yayin da ya kai wa dakarun kasar ziyara a fagen yakin da suke yi da ‘yan tawaye a cewar kakakin rundunar sojin Chadi.
Yanzu haka makomar kasar ta Chadi na cike da rashin tabbas.
Shugabannin ‘yan adawa da ‘yan tawayen da ake zargi da kashe Deby, sun ce ba su ji dadi ba saboda a cewarsu, dora dansa Mahamat Idriss Deby mai shekara 37 da dakarun kasar suka yi akan karagar mulki don ya jagoranci gwamnatin wucin gadi, tamkar juyin mulki ne.
Bayan an kammala jana’izar da addu’o’i a babban masallacin N’Djamena, an tafi da gawar Deby Amdjarass, wani kauye da ke da tazarar tafiyar kusan kilomita 1,000 (mil 621) daga babban birnin kasar domin a binne shi.
Labarai masu alaka
Zangon shirye-shirye
-
Nuwamba 04, 2024
Yaushe Ne Bakon Haure Yake Samun Damar Kada Kuri’a A Zaben Amurka?