An kaurace ma hanyoyin birnin kuma mazauna unguwannin sun katse hanyoyi don su kare unguwanninsu daga karin tashin hankali.
Shugaban Majalisin Birnin Trabulus, al-Sadat al-Badri ya ce kwanaki uku za a yi ana zanga-zangar.
Tashin hankalin ya barke ne ranar Jumma’a bayan da aka hallaka mutane akalla 43 wasu kuma 450 su ka sami raunuka, bayan da wasu ‘yan bindiga daga birnin Misrata su ka bude wuta kan masu zanga-zanga wadanda su ka yi macin don bayyana bukatarsu ta neman ‘yan bindigar su bar birnin.
An sami karin akalla wani mutum guda da ya rasu jiya Asabar yayin da wasu kuma da dama su ka sami raunuka, bayan da wani sabon tashin hankalin ya barke a babban birnin na Libiya, a yayin da sojoji da wasu masu dauke da makami da ke goyon bayan gwamnati su ka yi kokarin kawo kwanciyar hankali.
Firayim Ministan Libiya Ali Zidan ya gargadi ‘yan bindigar cewa kar su shiga birnin na Trabulus a yayin da yake kiran da akai zuciya nesa. ‘Yan sand aba su iya zuwa wasu sassan na unguwar Gharghour, inda nan ne tungar ‘yan bindigar da su ka taho daga Misrata tun asali su ke.