Ministocin harakokin wajen kasashen uku ne suka bada wannan jan kunnen yau Alhamis, inda har na Ingila ya nuna cewa ana sa ran a kai wasu daga cikin hare-haren akan wuraren da aka san turawan yammaci na yawan zuwa.
Wannan gargadin yana zuwa ne kwana daya bayanda sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton ta bada sheda a gaban majalisar dokokin Amurka kan farmakin da aka kai ran 11 ga watan Satumbar bara akan karamin ofishin jakadancin Amurka dake can Benghazi, inda a ciki har aka kashe jakadan Amurka Christopher Stevens da wasu Amurkawa ukku.