Wani bom ya tarwatse a harabar karamin ofishin Jakadancin Misra da ke kasar Libiya a birnin Benghazi da ke gabashin kasar a jiya Asabar. Fashewar ta lalata bangon rukunin ginin da wasu ababen hawa da ke kusa da wurin.
Masu bincike sun ce nan take dai babu wanda ya dau alhakin kai harin.
Haka zalika, masu kaifin kishin Islama da sauran masu zanga-zanga sun yi gangami a wurare da dama a yankin don nuna bacin ransu da yadda gwamnati ke gallaza wa fararen hula.
Dubban Larabawan da ke kasar Isira’ila sun yi ta kada tutocin kasar Misra da hoton Mr. morsi jiya Asabar yayin da su ke maci a birnin Nazareth da ke arewacin kasar.
Daruruwan mutane kuma sun taru a harabar ofishin jakadancin Misra da ke Tunis ranar Jumma’a inda su ka yi tir da yadda ake murkushe zanga-zangar.
Har ila yau kuma dubban mutane sun yin gangami a biranen Ankara da Istanbul na kasar Turkiyya, don nuna goyon bayansu ga masu zanga-zangar.
Kuma, dinbin kungiyoyin Musulmi sun yi maci a kasashen Indonesia da Malaysi inda su ka yi kira ga gwamnatin Misra da ta daina amfani da karfi fiye da kima kan masu zanga-zanga.