A karo na farko sakatariya Clinton ta bada shaida gaban kwamitin kula da harkokin kasashen waje dangane da harin da aka kai kan ofishin Amurkan dake Libya a ranar 11 ga watan satumban bara.
Cikin manyan masu sukar lamarin sakatariya Clinton, har da tsohon dan takarar shugabancin Amurka senata John McCain. Da yake magana shi ma senata Bob Corker, dan jam’iyyar Republican daga jihar Tennessee, yace gazawar da aka samu ta fuskar tsaro alama ce ta irin manyan matsaloli da ake fuskanta a ama’aikatar.