Shugaban Faransa Fransuwa Hollande yace gwamnati na sa ran jami’an Libiya zasu taimaka, wajen gano dalilin kai wannan hari, da kuma gurfanar da wadanda suka aikata hakan a gaban kuliya.
Ya kara da cewa ana kai harin bom ne ga duka kasarshen dake da hannu wajen yakar ta’addanci.
Kasar Libya dai na fama da tashe-tashen hankula da rashin kwanciyar hankali tun bayan da aka tunbuke shugabanta mai mulkin kama karya, kuma wanda ya dade akan karagar mulki Moamar Gadhafi a karshen shekata ta 2011.
Wani hari akan ofishin jakadancin Amurka dake Benghazi a watan Satumbar da ta wuce ya kashe jakadan Amurka da wasu Amurkawa guda 3.