Jami'ai sun ce mutumin da ake zargin, sunan shi Abu Anas el-Liby, kuma ranar asabar aka kama shi da ran shi a kusa da birnin Tripoli,a ksar Libiya cikin wani samamen hadin guiwar sojojin Amurka da jami'an leken asirin kasar.
Amurka ta yi bayanin samamen da ta kai ne jim kadan bayan da 'yan uwan Abu Anas dan shekaru Arba'in da Tara suka fara cewa an sace shi a birnin Tripoli.
Kamfanin dillancin Labaran Reuters ya ruwaito wani dan uwan shi ya na cewa an tafi da Abu Anas a lokacin da yake ajiye motar shi a kofar gidan shi da jijjifin asabar bayan sallar asuba. Ya ce wasu motoci uku suka zagaye shi, su ka fasa gilashin tagar motar shi, suka kwace makamin da yake dauke da shi sannan suka gudu da shi.