Majalisar Koli Ta Addinin Musulunci a Nijar ta ayyana yau Laraba a matsayin ranar Sallar "Eid el Fitr," wato karamar Salla ko Sallar Idi. Wannan ya biyo bayan ganin jaririn watan Shawwal a wasu garuruwan kasar, wanda ya kawo karshen azumin watan Ramadan.
Wakilin Sashin Hausa, Abdullahi Mamman Ahmadu, ya ce wajen karfe tara (9) na dare ne Hukumar Koli Ta Harkokin Addinin Musulunci ta tabbatar wa 'yan jarida labarin ganin jaririn watan Shawwal a garuruwan Bouza da Tera da yankin Zinder, wanda ya kawo karshen azumin kwanaki 29 da Musulmin kasar su ka yi su na azumi.
Wakilin Muryar Amurka ya garzaya kasuwanni da daren jiya, misalin karfe daya da rabi (1:30) na daren, inda ya tarar cewa farashin kaji da sauran abubuwa sun haura sosai. Wakilin na Sashen Hausa ya lura cewa bana dai Janhuriyar Nijar za ta yi Sallar Idi kafin makwabtan kasashe irin su Nijeriya da Libiya da kuma can kasar Saudiyya.