Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Fara Yunkurin Fadada Huldar Kasuwanci Da Nijar


Tawagar Rasha
Tawagar Rasha

Wata tawwagar mataimakin ministan tsaron kasar Rasha hade da ta ‘yan kasuwar Rashar sun kai ziyara a jamhuriyar Nijar inda suka gana da hukumomin mulkin sojan kasar a ci gaba da karfafa hulda a sabon kawancen da kasashen 2 suka kulla a washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.

Sai dai masana da kungiyoyin fafutuka na fatan ganin an yi abinda zai bai wa Nijar da jama’arta damar morar wannan alaka.

Batun tsaro na kan gaba a jerin fannonin da Nijar da Rasha suka kudiri aniyar karfafa hulda kansu a yarjejeniyar da suka cimma a yayin rangadin da mataimakin Ministan Tsaron Rashar, Kwanel-Janar Evkourov Lunus Bek, ya gudanar a birnin Yamai a watan Disamban 2023 dalili kenan ya dawo a karo na 2 da zummar kara jaddada abubuwan da aka tsayar .

Bayan ganawa da Janar Abdourahamane Tiani, tawagar Rashar ta yi wani zama da masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaron kasar a karkashin jagorancin Ministan Cikin Gida, Janar Toumba Mohamed, a madadin takwaransa na tsaro.

Abdourahamane Tiani
Abdourahamane Tiani

Nijar wace ke fama da aika aikar ‘yan ta’adda ta yanke shawarar kulla alakar kut da kut da Rasha a washe-garin juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023 a yunkurin neman mafitar wannan matsala, abin da kwararre akan sha’anin tsaro Abass Moumouni ke ganin ya na da fa’ida.

A baya bayan nan kasar ta juya wa Faransa da Amurka baya don rungumar Rasha da nufin samun mafita, amma Shugaban kungiyar fafutika ta FCR Souley Oumarou na cewa suna jiran gani a kasa.

Nijar kamar makwabtanta Mali da Burkina Faso na fama da hare hare daga kungiyoyin ta’addanci sama da shekaru 10 duk da dubban sojojin da kasashen yammaci suka girke a yankin sahel.

A ci gaba da fadada hulda da Nijar, kasar ta Rasha a karon farko ta turo wata tawagar masu zuba hannun jari wadanda suka tattauna da Firai Minista Lamine Zeine da wasu mukarrabansa.

Yaki da masu tafka ta’asa a yanar gizo da harkokin wayar sadarwa da ma’adanai da makamashi da tsaro sune fannonin da aka sanar cewa wadanan ‘yan kasuwa na da fatan zuba jari.

A yanzu haka wasu rahotanni na cewa ma’aikatar makamashin Atom ROSATOM ta kasar Raha ta fara yunkurin samun yardar ma’aikatar Nijar don ganin ta samu mashigar da za ta bata damar maye gurbin ORANO na Faransa a wuraren da kamfanin ya kwashe gomman shekaru yana hakar karfen uranium.

Saurari rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG