Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Ya Bai Wa Ukraine Damar Amfani Da Makaman Amurka Wajen Kai Hari Cikin Rasha


Shugaban Kasar Amurka Joe Biden
Shugaban Kasar Amurka Joe Biden

Shugaban Amurka Joe Biden a sakaye ya baiwa Kyiv damar harba makaman da Amurka ta kai musu cikin kasar Rasha, tare da sharadin cewa a kusa da kan iyaka da yankin da ke kusa da birnin Kharkiv na arewacin Ukraine kawai za a kai harin, in ji jami'an Amurka a ranar Alhamis.

WASHINGTON, D. C. - Hukuncin ya yi daidai da canjin manufofin Biden, wanda har ya zuwa yanzu ya ki barin Ukraine ta yi amfani da makamin Amurka wajen kai hare-hare a cikin Rasha.

"Kwanan nan shugaban ya umurci tawagarsa da su tabbatar da cewa Ukraine ta iya amfani da makaman da Amurka ta kawo wa yankin na Kharkiv domin Ukraine ta mayar da martani ga sojojin Rasha da ke kai musu hari ko kuma suna shirin kai musu hari," in ji wani ‘dan hukuma Ba'amurke.

Ofishin jakadancin Rasha dai da ke Washington da kuma tawagar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya a New York ba su amsa bukatar jin ta bakinsu ba.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG