Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Rasha Sun Koma Sansanin Sojin Saman Nijar Inda Wasu Sojojin Amurka Suka Rage


Russia - Sojoji
Russia - Sojoji

Wani jami'in Amurka ya fada a ranar Alhamis cewa Rasha ta tura wasu sojojinta zuwa wani sansanin sojin sama a Jamhuriyar Nijar inda wasu 'yan tsirarun sojojin Amurka suka rage bayan da akasarin sojojin Amurka suka fice daga sansanin da ke Yamai babban birnin kasar.

WASHINGTON, D C. Zuwan masu horaswa na Rasha a kasar da ke yammacin Afirka kimanin makonni uku da suka gabata ya biyo bayan matakin da Nijar ta dauka na korar dukkanin sojojin Amurka. Umurnin ya kawo cikas ga ayyukan sojojin Amurka a yankin Sahel, wani yanki mai fadi da ke kudu da hamadar Sahara inda kungiyoyi masu alaka da Al-Qaida da kungiyar IS ke gudanar da ayyukansu.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce sojojin na Amurka za su tashi amma ba ta ba da takamaiman lokaci ba.

Lokacin da sojojin Rasha suka isa Nijar a watan da ya gabata, ba a dai san inda suke ba. Wani jami’in Amurka ya ce yanzu haka suna can gefe daya na cibiyar Yamai da ake kira Airbase 101, kuma ba sa kusa da sojojin Amurka..

Filin jirgin yana kusa da filin jirgin sama na Diori Hamani, inda sauran sojojin kasa da kasa irin su Jamusawa da Italiya su ma suke zaune.

Jami’in ya yi magana ne bisa sharadin sakaya sunansa domin tattaunawa kan yunkurin dakarun.

Ba a bayyana takamaiman adadin sojojin Amurka da suka rage a sansanin na Yamai ba.

Kasancewar Rasha a sansanin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takun-saka tsakanin Washington da Moscow dangane da ci gaba da goyon bayan da Amurka ke bai wa sojojin Ukraine.

Kimanin sojojin Amurka 1,000 ne ke ci gaba da zama a Nijar, amma yawancinsu sun koma wani wuri da ake kira Airbase 201 da ke kusa da Agadez, mai tazarar kilomita 920 daga babban birnin kasar, ba da dadewa ba bayan da wasu sojojin Nijar suka hambarar da zababben shugaban kasar ta hanyar dimokuradiyya a watan Yulin da ya gabata.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG