Kafar talabijan RTN mallakar gwamnatin Nijer wacce ta ya nuna saukar jirgin a filin jiragen saman Yamai a ranar Asabar hudu ga watan mayu, tace tawwagar dakarun rashar na dauke da tallafin kayan aikin soja da kayan agaji. Wannan na faruwa a wani lokacin da hukumomin mulkin sojan CNSP ke kara bullo da matakan raba gari da kasashen yammacin duniya ciki har da Amurka.
Jirgin dakon kaya ne ya sauka filin jirgin saman Diori Hamani na birnin Yamai dauke da wasu sojojin rasha masu aikin horo da ba a bayyana adadinsu ba a ci gaba da karfafa huldar aiyukan sojan kasashen biyu, yunkurin da wani dan fafutika Hamidou Sidi Fody na kungiyar kulawa da Rayuwa ke ganin ya yi dai dai.
Karo na biyu kenan da gwamnatin Putin ke aikaswa da dakaru domin karfafa gwiwa ga sojojin Nijer a yunkurin neman mafitar matsalar tsaron da kasar ke fama da ita sanadiyar ta’addancin da ya addabi yankin sahel.
Baya ga kayan aikin tsaron, jirgin ya sauka da lodin kayan abinci a matsayin wata gudunmowa abin da kafar gwamnatin ta Nijer ta ayyana a matsayin wata alamar dake fayyace girman alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
La’akari da hakan ya sa kwararru gargadin gwamnatocin kasashen da a halin yanzu ke matukar dasawa da Rasha su canza salo domin morar wannan hulda fiye da abin da ta fara bayarwa.
Wannan shine karo na uku da Rasha ke aikawa da jirage dauke da lodin kayan aikin soja da tallafin abinci zuwa jamhuriyar Nijer a kasa da wata guda, kuma karo na biyu da take turo sojojinta masu aikin horo a wani lokacin da ake tsara jadawalin kwashe sojojin Amurka 1,100 dake yankin Agadez, kamar yadda hukumomin CNSP suka yi umurni a tsakiyar watan Maris.
Rahotannin karshen mako sun ce sojojin Rasha na zaune dab da inda wasu sojan Amurka ke girke wato filin jirgin sojan sama Escadrille dake birnin , wanda kuma nan ne sansanin da sojan Faransa suka zauna kafin a kore su daga kasar a karshen shekarar 2023.
Sakataren tsaron Amurka LIoyd Austin wanne ya tabbatar da wannan labari ya ce rayuwar dakaraun Amurka ba ta fuskantar kowace irin barazana a halin yanzu.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Dandalin Mu Tattauna