Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamus Za Ta Bar Sansanin Sojinta Na Nijar A Bude Bisa Yarjejeniyar Wucin Gadi - Berlin


Wasu Sojojin Kasar Jamus
Wasu Sojojin Kasar Jamus

Jamus za ta ci gaba da barin tashar sufurin jiragen samanta na soji a Yamai a bude a mataki na wucin gadi, kamar yadda ma'aikatar tsaro a Berlin ta bayyana a yammacin jiya Talata, jim kadan bayan da Tarayyar Turai ta sanar da kawo karshen aikin soji a kasar nan da ranar 30 ga watan Yuni.

WASHINGTON, D. C. - Berlin na da sojoji kusan 90 da ke Yamai a halin yanzu. Har zuwa juyin mulki a shekarar 2023, Nijar ta kasance kawa ga kasashen yammacin duniya da ke yaki da mayakan da suka kashe dubban mutane tare da raba wasu miliyoyi da muhallansu.

Sai dai kuma mahukuntan sojan kasar sun matsawa Faransa tsohuwar mulkin mallaka da ta janye dakarunta tare da amincewa da janye sojojin Amurka, inda ta kuma kara kulla alaka da Rasha.

Ma'aikatar tsaron Jamus a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce "Jamus da Nijar sun kulla yarjejeniyar wucin gadi da za ta ba da damar ci gaba da kasancewar sojojin Jamus a Nijar," in ji ma'aikatar tsaron Jamus, inda ta kara da cewa hakan zai baiwa Berlin damar bude sansanin tun daga ranar 31 ga watan Mayu a yanzu.

Tun a shekara ta 2013 ne dai Jamus ta yi amfani da sansanin da ke Yamai a matsayin cibiyar samar da kayan aiki ga dakarunta a makwabciyarta Mali inda suke aiki a cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, MINUSMA.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG