WASHINGTON, D. C. - Sama da shekaru biyu da barkewar wannan yaki mafi muni a nahiyar ta turai tun bayan yakin duniya na biyu, Putin ya sha yin gargadi kan yiwuwar kazancewar yakin yayin da kasashen yammaci ke nazarin yadda za a dakile kutsawar dakarun Rasha cikin Ukraine.
Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya shaidawa jaridar The Economist cewa, ya kamata mambobin kawancen su bar Ukraine ta shiga cikin kasar Rasha da makaman kasashen yamma, ra'ayin da wasu mambobin kungiyar NATO ke goyon baya amma ban da Amurka.
Putin ya fadawa manema labarai a Tashkent cewa: "Idan wadannan munanan sakamako suka faru a Turai, ta yaya Amurka za ta kasance, tare da la'akari da daidaiton mu a fagen makamai masu mahimmanci.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna