Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nyako Na Juyayin Korar Gulak


Murtala Nyako, gwamnan Jihar Adamawa
Murtala Nyako, gwamnan Jihar Adamawa

Gwamnan Jihar Adamawa mai fama da rigingimun siyasa, Murtala Nyako ya bayyana alhininsa gameda korar Ahmed Gulak.

A wani martanin da gwamnan jihar Adamawa ya mayar, biyo bayan sanarwar dakatar da Ahmed Gulak, dan asalin Jihar Adamawa, dake dauke da sa hannun mai bashi shawara akan harkokin yada labarai Mallam Ahmed Sajo, gwamnan yayi shagube ne akan cewa al ummar jihar, sun kadu da saukewar bazata da akayi wa Gulak.

Murtala Nyako yace ba hakan aka so ba, kana ya kara da cewa mutanen Jihar Adamawa zasu cigaba da alhini da juyayin sallamar da akayi masa, sannan ya shawarci masu rawa da murna a garin gulak da suyi hakuri su daina.

Kawo yanzu jam'iyyar PDP bata ce komai ba, gameda yadda shugabannin siyasa suka tarbi wannan labari, amma akwai rade-radin cewa Gulak na so ne ya tsaya takarar gwamnan Jihar a karkashin PDP.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG