Abati yace shugaba Jonathan ya gode ma Gulak a saboda ayyukan da yayi ma wannan gwamnati, ya kuma yi masa fatar alhaeri da nasara a ayyukansa na gaba.
Abati ya kara da cewa nan gaba za a ayyana wanda za a ba wannan mukamin.
Sauke Ahmed Gulak a matsayin mai baiwa shugaban kasa shawarwari akan harkokin siyasa, da ya fito akan shafukan yanar gizo, wanda kakakin shugaban Ruben Abati ya fitar yazo wa mutane da mamaki, ganin yadda Gulak ke kare muradun Jonathan.
Sashen Hausa na Muryar Amurka yayi kokarin jin ta bakin Gulak, amma bai samu nasara ba.
Sai dai kafin fitowar wannan sanarwa, wakilin Sashen Hausa, Nasiru Adamu El-Hikaya ya tattauna da Ahmed Gulak akan daukar mataki dangane da cire gwamnonin jihohin dokar-ta-baci.
“Bani da masaniya akan wannan batun. Wannan ba maganar PDP ko APC bane, maganar tsaro ne a kasa ya tabarbare,” a cewar Ahmed Gulak.
Mai taimakawa Gulak akan harkokin masarautu da addini Sunusi Baban Tanko ya bayyana korar Gulak din, yana mai cewa hakan bashi da nasaba da rashin jituwar Gulak, da gwamna Godswill Akpabio.