Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Ayyana Zaman Makokin Kwanaki 3 Bayan Kisan Sojojinta 29


Sojojin Nijar
Sojojin Nijar

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun ayyana zaman makokin kwanaki 3 daga ranar 3 ga watan Oktoba da nufin nuna alhinin rasuwar wasu sojojin kasar akalla 29, bayan wani hari da ‘yan ta’adda suka kai a ranar Litinin a kan iyakarta da Mali.

Sanarwar da aka bayar a kafar talabijin din RTN mallakar gwamnatin Nijar a tsakiyar daren Litinin, ta fadi cewa wani ayarin sojojin FAN ya fuskanci hari mai cike da sarkakiya a arewa maso yammacin Tabatole, inda maharan suka yi amfani da nakiyoyi da aka bizne a kasa hade da motocin da aka dana boma-bomai a jikinsu a daidai lokacin da wasu ‘yan ta’adda sama da 100 suka isa wurin a kan babura da motoci, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji da dama.

Sakamakon wucin gadi ya yi nunin cewa sojoji kimanin 29 ne suka rasu sannan wasu biyu suka ji mummunan rauni yayin da aka hallaka gomman ‘yan ta’addan tare da kona babura 15, sannan an kwato tarin bindigogi da albarusai.

Kutsen da aka yi a hirar wayar ‘yan bindigar da suka tsere a yayin wannan kafsawa ya bada damar gano cewa sun sami tallafin wasu kwararrun kasashen ketare wajen kitsa wannan ta’asa.

Domin nuna alhinin wannan babban rashi gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makokin kwanaki uku daga ranar Talata an kuma sassauta tutoci a ofisoshin gwamnati.

Matsalar tsaro a Nijar musamman akan iyakar kasar da kasashen Mali da Burkina Faso wani al’amari ne da za a iya cewa ana magani kai ya na kaba. Ko a ranar Alhamis din da ta gabata wasu sojojin kasar kimanin 12 sun kwanta dama a kauyen kandaji na Jihar Tilabery bayan wani babban gumurzu da aka yi da ‘yan bindiga.

Dan rajin kare hakkin jama’a Salissou Amadou na kungiyar Sauvons Le Niger, na mai bayyana takaicinsa kan abin da ya kira makarkashiyar da abokan gaba ke kulla wa wannan kasa.

A ci gaban wannan sanarwa hukumomi sun zargi wasu manyan kasashe da hannu a aika-aikar da kasar ta Nijar ke fuskanta koda yake ba a ambaci sunan kowace kasa ba. Suna masu kiran ‘yan kasa su kwantar da hankalinsu domin gwamnati za ta dauki dukkan matakan da suka dace wajen murkushe wannan makarkashiya da suka ce abu ne da ake tsarawa da hadin bakin wasu munafukai na ciki da wajen kasa.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Nijar Ta Ayyana Zaman Makokin Kwanaki 3 Bayan Kisan Sojojinta 29
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG