Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojan Nijar 6 Sun Rasu Yayinda Suka Hallaka 'Yan Ta'adda 31 A Wani Gumurzu


Sojojin Nijar
Sojojin Nijar

Hukumomin tsaron Jamhuriyar Nijer sun bada sanarwar kashe gomman ‘yan ta’adda yayinda sojoji 6 suka rasu wasu 18 suka ji rauni sakamakon gumurzun da aka yi a arewacin jihar Tilabery.

Yayinda wasu ‘yan kasar ke kallon abin a matsayin galaba akan abokan gaba wasu kuwa na gargadi mahukunta su kara zage damtse don tunkarar wannan al’amari da ke zama tamkar ana magani kai ya na kaba.

Lamarin ya faru ne a cikin daren Lahadi wayewar Litinin, 16 ga watan Oktoban 2023 lokacin da wasu dakarun tsaro na Operation Niyya da ke aikin sintiri a karkara Lemdou da ke a tazarar km 50 a arewa maso yammacin Tera suka yi kicibus da wasu ‘yan bindiga.

An dai dauki lokaci mai tsawo ana barin wuta inda sojojin Nijer suka yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda 31 koda yake sojoji 6 sun rasu wasu 18 suka ji rauni wadanda aka kwantar a wani asibitin Yamai kamar yadda aka bayyana a sanarwar ofishin ministan tsaron kasa.

Wani jami’in fafutika kuma mazaunin jihar Tilabery, Ibrahim Mamoudou ya jinjina wa sojojin Nijer abinda ya kira jajircewarsu a yaki da ta’addanci.

Sanarwar ta kara da cewa Baraden sun lalata babura 14 na ‘yan ta’adda sannan sun kwace bindigogi 6 kirar AK 47 da samfarin M80 1 . Wannan shine karon da ba adadi da ake fuskantar harin ta’addanci a jihar Tilabery a tsawon watanni biyu na baya bayan nan.

Jigo a kungiyar farar hula ta Sauvons le Niger, Salissou Amadou na mai yi wa hukumomi hanunka mai sanda game da abubuwan da ke wakana a garuruwan da ke makwafataka da kasashen Mali da Burkina Faso.

A wani labarin na daban da ke da nasaba da matsalar tsaro, rahotannin da ba na gwamnati ba sun ayyana cewa al’umomin kauyuka da dama na jihar Tilabery mai iyaka da Burkina Faso sun tsere daga matsugunansu don samun mafaka a garuruwan Tamou da Torodi bayan da ‘yan bindiga suka umurcesu su fice ko kuma su kuka da abinda ka iya biyo baya.

Wani bidiyo mai nasaba da wannan labari da aka wallafa a kafafen sada zumunta na nuna mata da yara kanana sun taru a farfajiyar wata makaranta da ke kama da sansanin ‘yan gudun hijira.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG