Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Bada Lasisin Hakar Ma'adinai Kawai Ga Kamfanonin Da Ke Aiki Cikin Kasar


Hakar Ma’adinai
Hakar Ma’adinai

Najeriya za ta ba da sabbin lasisin hakar ma'adinai ne kawai ga kamfanonin da suka gabatar da wani shiri kan yadda za a sarrafa ma'adanai a cikin gida, karkashin sabbin ka'idoji da ake samar da su, kamar yadda kakakin gwamnati ya tabbatar a ranar Alhamis.

WASHINGTON, D. C. - Wannan na nuni da cewa an samu sauyi daga tsarin da Najeriya ta kwashe shekaru da dama ta yi na fitar da albarkatun kasa zuwa kasashen waje yayin da gwamnatocin kasashen Afirka ke daukar matakai na fitar da karin kimar ma'adinan da suke da shi.

Hakar Ma’adinai
Hakar Ma’adinai

Domin karfafa zuba jari, Najeriya za ta baiwa masu zuba jari kwarin guiwa da suka hada da hana harajin shigo da kayan aikin hakar ma'adanai, da saukaka samun lasin na samar da wutar lantarki, da ba da damar mayar da cikakkiyar ribar da aka samu da kuma inganta tsaro, in ji Segun Tomori, mai magana da yawun ministan bunkasa ma'adanai na Najeriya.

Tomori ya ce, "Kafin musanya, dole ne mu sake duba shirinsu na kafa masana'antar da kuma yadda za su kara wa tattalin arzikin Najeriya daraja." Bai bayyana lokacin da za a kammala ka'idojin ko kuma za su fara aiki ba.

Sai dai a makon da ya gabata Ministan Ma’adanai Dele Alake, ya ce a yanzu manufar gwamnati ce ta sanya karin darajar ya zama sharadin samun lasisi ta yadda za a samar da ayyukan yi da kuma taimakawa al’ummomin yankin.

Alake, wanda kuma ke jagorantar wata kungiyar dabarun hakar ma'adinai ta Afirka da ta kunshi ministocin ma'adinai daga Uganda, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Saliyo, Somalia, Sudan ta Kudu, Botswana, Zambiya da Namibiya, na da kudirin yin wani yunkuri a duk faɗin nahiyar don samun mafi girman fa'ida daga cikin gida daga binciken ma'adinai.

Najeriya, wacce ke kan gaba wajen samar da makamashi a nahiyar Afirka, ta yi ta faman fitar da kimarta daga dimbin albarkatun ma'adinai da take da su, sakamakon rashin kuzari da kuma rashin kulawa. Bangaren hakar ma'adinai da ba a ci gaba ba yana ba da gudummawar kasa da kashi ɗaya cikin ɗari na dukiyoyin cikin gida na ƙasar.

A shekarar da ta gabata Najeriya ta fitar da ma'adinan dala da yawansu ya kai kimanin Naira biliyan 137.59 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 108.34, musamman zuwa kasashen China da Malaysia, kamar yadda hukumar kididdiga ta kasar ta bayyana.

Gwamnati na da burin kara zuba jari a fannin ta hanyar ba da wasu lasisi, inda ta kafa wani kamfani mai fa'ida na ma'adinai mallakin gwamnati wanda ke baiwa masu zuba jari kashi 75% na hannun jari tare da kafa wani sashin tsaro na musamman da ke da alhakin yaki da masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG