Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Rattaba Hannu A Yarjeniyoyi Da Dama Yayin Ziyarar Tinubu A Qatar


Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu da Sarkin Qatar, Mai Martaba Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Thani
Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu da Sarkin Qatar, Mai Martaba Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Thani

A jiya Lahadi ne, Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu da Sarkin Qatar, Mai Martaba Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Thani suka shaida  bikin rattaba hannu akan wasu yarjeniyoyi masu tarihin gaske tsakanin kasashen 2.

WASHINGTON DC - Al’amarin da zai bada damar cin gajiyar juna a muhimman fannonin da suka hada da ilmi, bunkasa kasuwanci da zuba jari, tallafawa matasa, hakar ma’adinai, yawan bude idanu da kuma wasanni.

Hadimin Shugaba Tinubu akan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi.

A cewarsa, gabanin bikin rattaba hannun daya gudana a fadar sarkin na Qatar, Shugaba Tinubu ya baiwa masu masaukin nasa tabbaci game da shirin Najeriya na marabtar masu sha’awar zuba jari zuwa cikin kasar, inda yayi tsokaci game da sauye-sauyen da gwamnatinsa ke gudanarwa da suka bada mahimmanci akan kirkire-kirkire da samun riba akan jarin da aka zuba da kuma yin mu’amala da mabambantan al’ummomi.

“Abun alfaharinmu shine al’ummarmu. Karfinmu na tattare ne da basirar matasan Najeriya. Zarata ne masu dimbin basira da yarda da kawunansu. Zasu kasance abokan hulda na gari ga kamfanonin qatar. Masu ilmi ne kuma abin dogaro, tunaninsu a kullum shine yadda zasu kawo ci gaba. ‘Yan tsiraru ba zasu bata sunan masu yawa ba. A Shirye matasan Najeriya suke su bada gudunmowa domin ci gaban kasashen 2.”

Bola Ahmad Tinubu da Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Thani
Bola Ahmad Tinubu da Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Thani

An ruwaito Sarkin Qatar yana cewar, “ya me girma shugaban kasa, ayyukanka da irin shaukin da kake da shi na samar da sabbin damammaki sun kara min kwarin gwiwa. Muna maraba da hakan, kuma a wannan gaba akwai bukatar a rika bibiya. Dukkaninmu mun muradin aiwatar da tsare-tsaren, saidai wajibi ne mu rika bibiya. San aika da tawagar jami’an kasarmu zuwa Najeriya bayan azumin Ramada, kuma zamu ci gaba da tattaunawa akan irin damammakin zuba jarin dake akwai.”

Nan Take, Shugaba Tinubu ya ayyana sunan Ministan Kudin da Tattalin Arziki, Mr. Wale Edun a matsayin shugaban tawagar jami’an gwamnatinsa da zasu yi aiki tare da hukumomin Qatar wajen gano damammakin zuba jarin da yadda za’a aiwatar dasu a nan gaba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG