Yarjeniyoyin da Najeriya zata kulla da kasar Kuwait zasu taimaka wurin samar da aikin yi da inganta harkokin kasuwanci. Jakadan Najeriya a kasar Kuwait Ambassador Haruna Garba yace Najeriya zata kulla yarjeniyoyi shida da kasar.
Tun shekarar 1981 aka bude ofishin jakadancin Najeriya a Kuwait wadda kasa ce karama amma tana da karfin tattalin arziki.
Kawo yanzu dai akwai 'yan Najeriya a fannin ilimin kasar ta Kuwait suna koyaswa da wasu kuma dake kasuwanci. Ban da haka 'yan Najeriya da yawa suna da ajiya a kasar ta Kuwait. Yanzu dai akwai 'yan Najeriya kusan dubu biyu da dari biyar mazauna Kuwait.
Yarjeniyoyi shidan da zasu kulla sun hada da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin kasashen biyu da na kasuwanci da dai sauransu.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.