Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Sunusi Lamido Sunusi a Zaman Sabon Sarkin Kano


Sanusi Lamido Ado Bayero, Yuni 7, 2014.
Sanusi Lamido Ado Bayero, Yuni 7, 2014.

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya gaji kujerar marigayi. Alhaji Ado Bayero.

An nada tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Sunusi Lamido Sunusi, a zaman sabon Sarkin Kano.

Sakataren gwamnatin Jihar Kano, Injiniya Rabi'u Sulaiman Bichi, shi ya bayar da sanarwar nadin na Sunusi Lamido Sunusi, kwana biyu bayan rasuwar Alhaji Ado Bayero.

Tun da fari, an yi ta yada jita-jita a kafofin zumunci na intanet cewar an nada Chiroman Kano, Alhaji Sunusi Lamido Ado Bayero, babban dan marigayi, abinda har sai da gwamnati ta fito ta karyata wannan labarin.

Sabon sarkin na Kano dai sanannen ma'aikacin banki ne wanda ya shahara har ya zamo gwamna na babban bankin Najeriya.

Kwanakin baya, ya shiga takun saka da gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan, a kan wasu kudaden da yayi zargin cewa sun bace a ma'aikatar man fetur. Wannan takaddama ta sa gwamnati ta tube shi daga kan mukaminsa.
XS
SM
MD
LG