Matakinda rundunar sojojin Najeriyan ta fara dauka tun ranar jumma'a yafi shafar jaridun Daily Trust da Leadership da kuma jaridar The Nation, amma yanzu matakin ya shafi kusdan dukkan jaridun kasar.
Da yake magana da wakilin Sashen Hausa kan wannan mataki babban editan jaridar Daily Trust Munir Dan Ali, yace zuwa yanzu dai babu wata hukumar soja ko ta wata jami'an tsaro da suka tuntube su domin bayyana na musu dalilin daukar wannan mataki. Munir yaci gaba da cewa "idan batun tsaro ne, me yasa idan suka kammala duba duba motocin, kuma basu gano komi ba, duk da haka suke hana jigilar jaridun".
Da aka tambayeshi ko yana ganin wannan mataki ba zai rasa nasaba da rahoto kan wantarda ake zargi manyan hafsoshin kasar suka yi da fulotai da aka kebe na musamman domin gina barikin soja a unguwar Asokoro dake Abuja, Munir yace ai sojojin basu musanta sunyi hakan ba.
Ga karin bayani.