Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanadiyar Hare-haren Boko Haram Yanzu Mata ke Binne Matattu a Gwoza


Marigayi sarkin Gwoza Alhaji Shehu Idris Timta da 'Yan Boko Haram suka kashe.
Marigayi sarkin Gwoza Alhaji Shehu Idris Timta da 'Yan Boko Haram suka kashe.

Yayin da kungiyar Boko Haram ke farautar maza a yankin Gwoza wadanda suka tsira da ransu sun gudu sun bar mata da binne matattu.

Dubban mutane ne a yankin Gwoza dake jihar Borno suka shiga wani halin lahaula walakawati sakamakon rashin ruwan sha da rashin abinci da kuma munanan raunuka da wasu ke fama dashi sabili da yawan hare-haren da 'yan Boko Haram ke kaiwa yankin ba dare ba rana.

Tun lokacin da gwamnatin Jonathan ta sabunta dokar ta baci kungiyar Boko Haram ta kara kaimi akan hare-haren da take kaiwa a jihohin dake cikin dokar. Kungiyar ta fi kai hare-haren a kauyuka inda take cin karenta ba babbaka.

Yawan hare-haren yasa masu ruwa da tsaki a yankin Gwoza sun kira taron gaggawa domin bullo da hanyar da za'a bi a tallafawa wadanda suka fice daga kauyukansu zuwa garin Maiduguri. Banda wadanda suka gudu akwai wadanda suna nan rai hannun Allah da yanzu haka suna nan baje a cikin daji.

Sanata Mouhammed Ali Ndume dan asalin yankin Gwoza shi ya jagoranci taron gaggawan. Yace akwai mutane da dama da suka gudu suna cikin dutse. Yunwa ta addabesu. Basu da ruwa, basu da abinci babu kuma maganin kula dasu. Yanzu yara ma suna mutuwa sanadiyar rashin ci da sha. Sanata Ndime yace taron na neman kayan agaji ne domin a taimaki wadanda basu da abin da zasu ci.

Kodayake kawo yanzu ba'a san adadin wadanda suka rasa rayukansu ba amma suna da dama. An kashe mutane da yawa. An kone gidaje masu dimbin yawa an kuma wawure dukiyoyi. Idan Sojoji sun samu sun shiga kauyukan ana iya samun alkaluman wadanda suka rasa rayukansu.

Lawanin kauyen Attagara cikin karamar hukumar Gwoza sun ce akwai yara da mata akan duwatsu sun kasa sauka ga kuma yunwa da suke fama da ita. Gawarwaki ma sun fara rubewa. Matan da suke taimakawa wurin binne matattu su ma basu iya shiga wasu wurare ba.

Sabili da rashin maza a garin mata su ne ke binne matattu domin ana farautar maza. 'Yan Boko Haram basu ware Kirista daga Musulmai ba. Duk sun hadasu suna kashewa.

Akwai wasu kauyuka 13 a Kwandiga da Jeri inda kawo yanzu 'yan Boko Haram na cigaba da kai masu hare suna karkashe mutanen wuraren.

Ga rahoton Haruna Dauda Biyu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG