Sakataren gwamnatin jihar Kano Alhaji Rabiu Suleiman Bichi yayin da yake bayyana sunan sabon sarkin yace masu zaban sarki sun zauna sun baiwa gwamnati shawara kuma gwamnati ta amince da shawarsu. Sabili da haka wanda aka zaba ya maye gurbin sarkin da ya rasu shi ne Sanusi Lamido Sanusi tsohon gwamnan babban bankin Najeriya.
Malam Sanusi Lamido Sanusi jikan sarkin Kano Sanusi ne. An haifeshi a ranar 30 ga watan Yuli 1961. Bayan yayi karance karabce na ilimin addini da na zamani ya fara aikin banki a shekara 1984 inda ma har ya kai kololuwa a fannin yayin da shugaban Najeriya marigayi Shehu 'Yaradua ya nadashi gwamnan babban bankin Nageria a shekarar 2009.
Bayan ficen da yayi a bangaren aikin banki sabon sarkin Sanusi Lamido Sanusi ya karantun ilimin shari'a inda ma ya samu digiri akan fannin shari'a daga Jami'ar Khartoum kasar Sudan a shekarar 1997. Bara ya zama dan majen Kano.
Tuni dai al'ummar kanawa suka fara tofa albarkacin bakinsu dangane da nadin sabon sarkin. Wasu da aka tambaya akan nadin sabon sarkin sun ce basu da abun da zasu fada. wasu kuma suna ganin kamata yayi a baiwa dan sarkin Kano sarautar Kano. Wasu kuma sun ce sanarwar zaban sabon sarkin ta sabawa abun da mutanen gari suka bukata lamarin da ya jawo hatsaniya a cikin gari. Wasu kuma gani suke gwamnati ta sake duba abun da tayi domin suna ganin yakamata a ba dan sarkin Kano da ya rasu wanda ya kwashe shekara 51 yana mulki. Wani yace bai ji dadi ba domin yakamata a ba dan wanda ya rasu. Wasu kuma cewa suka yi basa goyon bayan sabon sarkin.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.