Samarda taimakon shi ne jigon taron kungiyar Izala na shekara-shekara da a keyi a Abuja a cikin tunkarar watan azumi kasa da wata daya nan gaba.
Malamai a taron sun caccaki masu sako-sako da fitar da zakka da sauran al'adun marowata inda kungiyar ta nanata wani shirinta na samun wani shirin dogaro ga kai mai taken "Manara" wanda zai taimaka wajen yada ilimi da tallafawa rayuwar marasa galihu da tallafawa 'yan agaji.
Sheikh Abdullahi Bala Lau shugaban kungiyar yayi karin bayani. Yace suna da masallatai sama da dubu tara domin shirin Manara. Idan akwai wanda yake son ya tallafa yayi anfani da masallatan. Yace suna maraba da duk wata sadaka. Idan kuma mutum nada kayan da yake so a sayar masa kamar shinkafa zai kawo masallatan amma zai rage farashin kayan a watan azumi. Sheikh Lau yace tallafawar ba wai sai maraya musulmi ba. Duk wanda aka san maraya ne ko menene addininsa za'a tallafa mashi.
Yace idan aka koma ga Allah ana taimakawa marayu Allah na iya jin tausayin kasar ya kawar mata da bala'in da ta shiga.
Yanzu kungiyar ta mika takardun tura malamai sassa daban-daban domin tafsirin azumi.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.