Mr. Smith, yace ya zo Najeriya a bisa wakilcin kwamitin sa domin tattara bayanai da suka shafi fataucin mata a Najeriya, da kuma bada taimakon daya kamata domin kwato ‘yan mata Chibok.
Yace ya gana da ‘yan majalisun Najeriya da wadansu shuwagabanin addinai, kuma ya samu bayanai sosai saida yace an lura cewa ta’addanci na karuwa a duniya maimakon raguwa duk da kokarin da akeyi wajen magance shi.
Mr. Smith yace zai mika rahoton sa ga kwamitin su bayan ya koma Amurka domin nazari,amma yace alhakin kwato ‘yan mata na gwamnatin Najeriya ne.