Shugaban kungiyar matasan BACE na kasa da kasa, Mr. Dauda Aku ya ce matasan sun gamu da ajalinsu ne yayinda ruwa ya mamaye ramin da suke ciki suna neman ma'adinan kuza.
Malama Raulatu Piwuna, shugabar kungiyar mata dake aikin ma'adinai a jahar Filato, ta shawarci hukumomi da su tallafa wa matasan su kafa kungiyoyi don gudanar da aikin cikin tsari.
Kokarin ji daga bakin shugaban karamar hukumar Bassa, Mr. Joshua Riti ya ce tura.
A halin da ake ciki kuma, rundunar 'yan sandan jahar Filato to bukaci jama’a da su yi fatali da rahotannin tashin bam a cikin garin Jos, dake yawo a kafafen sada zumunta.
Rundunar ta ce jami'an ta sun binciko ramin da ake rade-raden cewa an dasa bam, kuma sun tona amma ba su sami komai ba, don haka suka bukaci jama’a su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:
Dandalin Mu Tattauna