Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama ‘Yan China 3 Da ‘Yan Najeriya 2 Kan Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba


'Tan China da 'yan Najeriya da aka kama
'Tan China da 'yan Najeriya da aka kama

An kama wadanda ake zargin ne a wani wurin hakar ma’adinai ta barauniyar hanya dake yankin Rafin-Gabas, Agwada, a karamar hukumar Kokona ta jihar.

An kama wasu ‘yan China 3 da wasu ‘yan Najeriya 2 akan hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar Nasarawa, a cewar gwamnatin tarayyar Najeriya.

Ministan Bunkasa Ma’adinai, Dele Alake, ne ya bayyana hakan a sanarwa da mai magana da yawunsa, Segun Tomori, ya fitar a jiya Litinin a Abuja.

Yace an kama wadanda ake zargin ne a wani wurin hakar ma’adinai ta barauniyar hanya dake yankin Rafin-Gabas, Agwada, a karamar hukumar Kokona ta jihar.

“An kama wadanda ake zargin ne saboda hakar ma’adinai ba tare da izini ba. Wasu daga cikin ma’adinan da aka hakar sun hada fluorite da zinc da dalma da kuma kuza,” a cewar Alake.

Ya kara da cewar kamfanin dake da hannu a lamarin ya fara aiki ne a 2021, abinda ya haddasawa gwamnatin Najeriya katafariyar asarar kudaden shiga.

Askarawan yaki da hakar ma’adinai ta barauniyar hanya, da aka kirkira domin kare wuraren hakar ma’adinai dake fadin Najeriya ne, suka gudanar da kamen sakamakon samun sahihan bayanan sirri.

Ministan ya kara da cewar, kawo yanzu an kama masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba fiye da 200, inda kimanin 140 daga cikinsu ke fuskantar shari’a a fadin Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG