A Larabar data gabata, Mai Shari’a Evelyn Anyadike ta babbar kotun tarayya dake ilori, ta yankewa wasu ‘yan China 2; Duan Ya Hong da Xiao Yi, hukunci zaman gidan kaso na shekara guda akan laifuffukan da suka shafi hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da kuma mallakar ma’adinan ba tare da cikakken lasisi ba.
Dukkaninsu sun amsa laifin tuhumar da aka karanto musu.
Sakamakon haka, an bada belinsu akan Naira milyan 5 da mutane 2 da zasu tsaya musu suma akan naira Milyan 5 kowanensu.
Har ila yau, kotun ta umarci Hukumar EFCC ta cigaba da tsare mutanen har sai sun kammala cika ka’idojin bada belin.
Daga nan kuma, kotun ta dage zamanta zuwa ranar Talata 14 ga watan Mayun da muke ciki domin yanke hukunci.
Bayan cikar wa’adin, ‘yan Chinar wadanda suka kasa cika ka’idojin bada belin, suka amince su amsa aikata daya daga cikin tuhume-tuhume 11 da ake yi musu tare da kin amsa ragowar, inda hakan ya tilastawa kotun dage zamanta zuwa Laraba domin sake nazarin hujjoji da kuma zartar da hukunci.
Bayan da kotun ta sake zamanta a ranar Larabar, lauyan EFCC, Innocent Mbachie, yayi nazarin hujjojin, tare da mika bayanan wadanda ake kara da hotunansu da kuma samfurin ma’adinan da babbar motar da suke amfani da ita da kuma rahoton binciken kwakwaf daga Hukumar Nazarin Duwatsu ta Najeriya domin yin sharhi kan ma’adinan.
Wadanda ake karar, da lauya I.A Ahmad ke wakilta, basu kalubalanci hujjojin da bangaren masu kara ya gabatar ba, don haka kotun ta karbesu.
Da take yanke hukunci, Mai Shari’a Anyadike ta bayyana cewar bangaren masu kara ya gabatar da hujjoji na yankan shakku tare da ayyana ‘yan Chinar a matsayin masu laifi akan tuhumar da ake yi musu.
Dandalin Mu Tattauna