Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Ta Soke Lasisin Kamfanin Kasar Kanada Dake Aikin Hakar Ma’adinan Uranuim


Uranium
Uranium

Gwamanatin mulkin sojin Nijar ta soke lasisin kamfanin kasar Kanada na GOVIEX dake gudanar da wani aikin habbaka hakar uranium a arewacin kasar.

Ma’aikatar kula da ma’adinai ta Nijar ce ta an sanar da kamfanin na Goviex mallakin kasar Kanada cewa daga yanzu bashi da wani sauran izini na ci gaba da aikin hakar ma’adinan Uranuim a madawela dake arewacin kasar wanda yanzu ke karkashin mallakin al’umma.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar ya bayyana cewa yana da 'yancin da zai ba shi damar kalubalantar matakin gwamnatin Nijar na soke lasisin sa na hakar ma’adinan a gaban kwararrun kotun cikin gida da na kasa da kasa.

Kuma wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da kamfanin ke shirin karbar bashin dala miliyan 200 domin gudanar da aikin sa na hakar ma’adinan a arewacin Nijar.

To sai dai kungiyoyin dake sa ido kan yadda ake hako arzikin ta bakin Abdoulaye Mohamed na ganin wannan matakin da gwamnatin Nijar ta dauka abin a yaba mata ne, shi kuma a nasa bangare Traore Hamidou na ganin akwai bukatar a tattauana tsakanin kamfanin da gwamnatin Nijar domin samar da hanyoyin magance wannan matsalar.

Masu fashin baki irin su Abdourahamane Dikko na alakanta wannan soke-soken lasisin kamfanonin Turai da gwamnatin mulkin sojin Nijar ke yi da sabuwar alakar dake tsakanin kasar ne da Rasha.

Kungiyoyin farar hula sun bukaci gwamnatin Nijar da ta mallakawa kamfanoni na cikin gida lasisin hakar ma’adinan maimakon kamfanonin kasashen ketare.

Kasar Nijar na da arziki mafi kyawun ma’adinan Uranium a Africa kuma ita ce kasa ta bakwai ajerin kasashen da ke kan gaba wajen samar da Uranium a fadin duniya.

Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:

Gwamnatin Nijar Ta Soke Lasisin Kamfanin Kasar Canada
Dake Aikin Hakar Ma’adinan Uranuim
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG