Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla 49 Sun Mutu Sanadin Nutsewar Kwale-kwale A Yankin Tekun Yemen


Hadarin Kwale-kwale
Hadarin Kwale-kwale

Wani kwale-kwale da ke dauke da bakin haure ya nutse a yankin tekun Yemen, inda mutane akalla 49 suka mutu, yayin da wasu 140 suka bace, a cewar hukumar kula da baki 'yan cirani ta Majalisar Dinkin Duniya da ake kira IOM a ranar Talata.

WASHINGTON, D. C. - Hukumar ta bayyana cewa jirgin na dauke ne da ‘yan Somaliya da 'yan kasar Habasha kusan 260 daga arewacin gabar tekun Somalia, inda suka yi tafiya mai nisan kilomita 320 a yankin tekun Aden a lokacin da ya nutse a kudancin gabar tekun Yemen a ranar Litinin.

An ceto mutane saba'in da daya kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a cewar hukumar, ta kuma kara da cewa mata 31 da kananan yara 6 na daga cikin wadanda suka mutu.

Tekun Yemen dai wata babbar hanya ce da bakin haure daga yankin gabashin Afirka ke bi, a kokarinsu na isa kasashen yankin Gulf domin samun aiki. Duk da yakin basasar da aka kwashe kusan shekaru goma ana yi a kasar Yemen, adadin bakin haure da ke isa yankin ya linka har sau uku a shekarun baya-bayan nan, daga kimanin 27,000 a shekarar 2021 zuwa sama da 90,000 a bara, in ji hukumar ta IOM a watan Mayu.

Kimanin bakin haure 380,000 ne ke kasar Yemen a halin yanzu, a cewar hukumar.

Don isa kasar Yemen, yawancin lokuta masu safarar mutane na kasadar daukar bakin a cikin kananan jiragen ruwa da ke cike da jama'a su bi ta tekun Bahar Maliya ko Tekun Aden. A cikin watan Afrilu, akalla mutane 62 suka mutu sakamakon kifewar jiragen ruwa guda biyu a gabar tekun Djibouti a lokacin da suke kokarin isa kasar Yemen.

Hukumar IOM ta ce akalla mutane 1,860 ne suka mutu ko kuma suka bace a kan hanyar, ciki har da wasu 480 da suka nutse.

Kifewar jirgin ruwan da ta faru ranar Litinin wani abin tunatarwa ne game da buƙatar gaggawar ta yin aiki tare don magance ƙalubalen ƙaurar baki da kuma tabbatar da tsaro da kariyar bakin haure a kan hanyoyin da suke bi," in ji kakakin hukumar IOM Mohammedali Abunajela.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG